Rikici ya barke a garin Kidal na Mali

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan tawayen Azbinawa a Kidal

Fada da manyan bindigo ya barke a garin Kidal a arewacin Mali.

Garin na Kidal nan ne inda 'yan tawaye ke da karfi, sai dai sojoji Malin suna sa ran sake kwato shi.

A ranar Litinin 'yan tawayen suka sako mutane ashirin da takwas da suka yi garkuwa da su lokacin ziyarar da Firaminista Moussa Mara ya kai a ranar Asabar.

Wani boren Abzinawa a arewacin Malin a shekarar 2012 ya haifar da juyin mulki.

A bara ne kuma aka sake maido da mulkin farar hula bayan da Faransa ta sa hannu domin kwantar da tarzoma, sai dai tun daga wannan lokacin, masu kishin Islama da kuma 'yan aware suna nan da karfi a wasu wurare.

Karin bayani