Kotu ta yanke wa Mubarak daurin shekaru 3

Hosni Mubarak
Image caption Masu shigar da kara sun ce sun yi amfani da kudaden ne wajen gyara gidajensu na kashin kansu

Wata kotu a Masar ta yanke wa tsohon shugaban mulkin sojin kasar Hosni mubarak, hukuncin shekaru uku a gidan kaso, saboda samunsa da laifi aikata almudahana.

Haka kuma 'ya'yansa maza biyu Alaa da Gamal, suma kotun ta yanke musu shekaru hurhudu a gidan maza, bisa aikata sama-da-fadi.

Masu gabatar da kara sun ce sun sauya akalar dala miliyan 17 a cikin shekaru goma, kudin da ya kamata a gyara fadar shugaban kasar.

Kotun ta kuma umarce su da su biya kudaden, sannan za su biya tarar kusan dala miliyan uku.