Chibok: Amurka ta tura sojoji Chadi

'yan matan Chibok Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'yan matan Chibok

Amurka ta aika sojoji zuwa kasar Chadi, a kokarin da kasashe ke yi na gano 'yan matan Chibok su fiye da 200 da Boko Haram ta sace.

A cikin wasikar da ya aike wa majalisar dokokin Amirka, shugaba Barack Obama ya ce, sojojin Amurkan su kimanin tamanin, zasu taimaka wajen tattara bayyanan sirri, da sa-ido, da kuma yin shawagi da jiragen leken asiri a arewacin Najeriya.

Fiye da makonni biyar kenan da 'yan Boko Haram din suka sace daliban 'yan mata daga makarantarsu.

Kasashe dayawa da suka hada da Birtaniya da Isra'ila na taimaka wa sojojin Najeriya da kwarewarsu ta fuskar leken asiri don gano 'yan matan.