An gano wata mata da aka sace a California

Hakkin mallakar hoto SANTA ANA POLICE
Image caption Saurayin wata mata ya sace 'yarta ya tilasta aurenta

Wata mata da ta bace a kudancin Carlifornia shekaru goma da suka wuce, ta kira 'yan sanda ta kuma shaida musu cewa sace ta aka yi.

'Yan sanda sun ce mutumin da ya sace ta Isidro Garcia mai shekaru 41 saurayin mahaifiyarta ne da suke zaune tare.

Ana tuhumarsa da laifin satar mutum, da aikata Fyade da kuma boye ta da ya yi.

Matashiyar wadda mahaifiyarta ta sanar da bacewar ta tun a shekarar 2004 ta shaidawa 'yan sanda cewar Mr Garcia ya yi amfani da muzugunawa dan hana ta guduwa.

Rahotanni sun bayyana cewa ta nemi taimakon 'yan sanda ne bayan ta gano 'yar uwarta a shafin sada zumunta wato Facebook.

Karin bayani