Mahaifiyar dalibar Chibok ta rasu

Hakkin mallakar hoto isa gusau
Image caption Wasu daga cikin daliban da suka kubuta

Mahaifiyar daya daga cikin 'yan matan da aka sace a Chibok da ke jihar Borno ta rasu sakamakon ciwon hawan jini.

Daya daga cikin iyayen 'yan matan ya shaidawa BBC cewar, matar ta rasu ne saboda shiga cikin damuwa na rashin tabbas game da makomar diyar ta.

Matar ta rasu ne a ranar Lahadi a yayinda aka birne ta a ranar Litinin.

Bayanai sun nuna cewar iyayen 'yan matan kusan uku zuwa hudu sun kamu da ciwon hawan jini tun bayan da aka sace musu 'ya'yansu a makarantarsu da ke Chibok.

Makonni biyar kenan da 'yan Boko Haram suka sace dalibai fiye da 200 inda kungiyar ta yi barazanar sayar da su a kasuwa.

Kasashen Amurka da Birtaniya da Isra'ila da China da kuma Faransa sun aika tawaga zuwa Nigeria domin taimakawa a ceto 'yan matan.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daliban da ke hannun Boko Haram
Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Abubakar Shekau

Karin bayani