Zanga zangar neman a ceto 'yan matan Chibok

Hakkin mallakar hoto AP

A Najeriya daruruwan 'yan kungiyar nan ta BringBackOurGirls, masu fafitikar ceto 'yan matan Sakandaren Chibok sun yi zanga-zanga ta musamman, don mika kokensu ga shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan.

Kungiyar dai ta nuna rashin gamsuwa da yunkurin da gwamnati ke yi na ceto 'yan makarantar.

'Yan sanda sun datse hanya sun hana masu zanga zangar danganawa da fadar Shugaban.

A ranar 14 ga watan Afrilu ne kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan su fiye da 250 daga makarantarsu da ke jahar Borno.

A cikin wata sanarwa, fadar Shugaba Goodluck Jonathan ta ce gwamnati na iya kokarinta don ganin an sako 'yan matan.

Gobe shugaba Jonathan zai je Afirka ta Kudu, inda zai tattauna tare da sauran shugabannin Afirka a kan yaki da ta'addanci a nahiyar