Minista ya kashe kansa a Malawi

Masu kada kuri'a
Image caption Wakilin BBC ya ce na'urar tattara kuri'un ta lalace a wasu gurare, saboda haka ana tattara takardun ne

Wani minista a Malawi ya harbe kansa a gidansa, yayin da kasar ke dakon sakamakon zaben shugaban kasa.

A cewar rundunar 'yan sandan kasar, mataimakin ministan harkokin kananan hukumomi mai barin gado, Godfrey Kamanya ya harbe kansa ne a gidansa.

Mr. Kamanya ya bar wasiyya cewa shugabar kasar Joyce Banda ta kula da 'yarsa tare daukar dawainiyar karatunta.

Mai magana da yawun mamacin ya musanta cewa, ministan ya kashe kansa ne saboda zai rasa mukaminsa.