Za a sanya Boko Haram cikin 'yan ta'adda

Wakilan Amurka da Burtaniya a kwamitin Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Najeriya za su zuba ido suka tasirin ayyana Boko Haram a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, idan hakan ta faru

Majalisar Dinkin Duniya za ta yanke shawara kan bukatar da gwamnatin Nigeria ta gabatar mata, ta ayyana kungiyar Boko Haram a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Kasar ta gabatar da bukatar yin hakan ne a gaban Kwamitin sulhu na Majalisar, wanda zai yanke shawarar a ranar Alhamis.

Idan har Majalisar ta amince da bukatar, to kasashe mambobinta za su samu damar taka-birki ga harkokin kungiyar Boko Haram, musamman abin da ya shafi asusun ajiyar kudi da makamai.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya riga ya nemi kasashen duniya, su sanya duk takunkumin da suka dake kan kungiyar da shugabanninta, domin murkushe kungiyar.