Za a ci gaba da tattaunawa a Thailand

Shugaban hafsan sojojin Thailand Janal Prayuth Chan-o-cha Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin dai sun ce ba juyin mulki su ka yi a kasar ba.

Nan gaba a yau ne jam'iyyun siyasa, da shugabannin masu zanga-zanga a kasar Thailand za su hadu domin sake tattaunawa dan kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar.

A jiya laraba ne aka kira taron gaggawa tsakanin wakilan gwamnati, da babbar jam'iyyyar adawa da kuma shugabannin masu boren kin jinin gwamnati sai dai an tashi dutse hannun riga.

Babban hafsan sojin Thailand Janal Parayut Chan-o-cha ya shaidawa mahalarta taron su koma teburin sulhu domin tabbatar da hanyoyon da za a gudanar da zabe, da sauye-sauye da kuma ko kasar ta na bukatar a nada sabon Prime Minista.

Sai dai wani mai zanga-zanga yace za su ci gaba da fafutukar da su ke yi har sai an samu sabuwar doka a kasar.

A ranar talatar da ta wuce ne sojojin Thailand suka ayyana dokar ta baci, tare da nanata cewa ba juyin mulki sukai a kasar ba.