An sanya Boko Haram a jerin 'yan ta'adda

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar Boko Haram dai ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, tun bayan fara kaddamar da hare-haren ta a arewacin Najeriya.

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sanya kungiyar Boko Haram a cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya.

Abin da ke nufin an haramta musu yin tafiya-tafiye, da hana su taba kadarorinsu, sannan ba za a sayar musu da makamai ba.

Matakin ya zo ne makonni shida bayan da Boko Haram kungiyar ta sace dalibai 'yan mata fiye da 200 a makarantarsu da ke garin Chibok a jihar Borno.

Amurka ta ce matakin Majalisar na da matukar muhimmanci, a kokarin da ake yi na taimakawa Najeriya murkushe kungiyar ta Boko Haram.

Karin bayani