Facebook zai fitar da sabuwar haja

Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Cikin makonnin da ke tafe tsarin zai soma aiki

Facebook ya ce zai fitar da wani sabon tsari na sauraron sauti da kuma kallon bidiyo a shafinsa na wayar salula.

Idan har wakar ko bidiyon suka yi daidai da manhajar Facebook din, to mutum zai iya wallafa shi kai tsaye a shafinsa ko kuma na abokansa.

Tsarin da za a samar a 'yan makonnin da ake tafe, zai dunga amfani da abun sauraro na jikin wayar salula ne.

A cewar Facebook mutum zai iya kashe tsarin ko kuma ya bar shi a kunne, sannan kuma sautin da aka nada ba zai bayyana asalin inda aka soma shi ba.

Kamfanin Facebook din ya ce wannan tsarin zai saukakawa miliyoyin mutane da ke musayar wakoki da shirye-shirye talabijin a dandalin.

Sabon tsarin kuma zai nuna tarihin mawaki da salon waka da kuma abubuwa makamanta haka.

Karin bayani