ICC ta yanke wa Katanga shekaru 12 a kurkuku

Germain Katanga
Image caption Germain shi ne mutum na biyu na kotun ta taba samu da laifi tun da aka kafa ta a shekarar 2002

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya, ICC ta yanke wa tsohon madugun yakin Congo, Germain Katanga hukuncin shekaru 12 a kurkuku.

A watan Maris da ya gabata ne aka samu Katanga da laifin hada baki domin kisan daruruwa mazauna kauyen Ituri, a lardin da ke da arzikin zinare a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Alkalin ya ce maharan sun yi gunduwa-gunduwa da mutane kafin su kashe su, a yunkurin kawar da kauyen daga doron kasa.

Wakilin BBC ya ce mutane da dama za ga hukunci a matsayin mai sassauci, amma alkalin na ganin akwai yiwuwar ya tuba, ganin yana da kuruciya lokacin da lamarin ya faru, kuma yana da 'ya'ya shida.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba