Musayar wuta da 'yan bindiga a Katsina

Image caption Dakarun tsaron Nigeria

Jami'an tsaron a jihar Katsina da ke arewacin Nigeria sun yi musayar wuta da wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne a Unguwar Filin Folo a babban birnin jihar.

Da safiyar yau aka yi bata kashin, inda wasu majiyoyin soji suka bayyanawa BBC cewar an kashe mutane biyu cikin 'yan bindigar.

Wani dan jarida a Katsina ya ce mutane hudu ne aka kashe kuma an kai gawawwakinsu zuwa asibitin gwamnatin Tarayya da ke Katsina.

Kwamandan Sojan Nigeria a Katsina, Laftanar Kanar Alhassan Grema ya shaidawa BBC cewar sun kai farmaki kan gidan da 'yan bindigar ne bayan samun wasu bayanan sirri game da shigowar 'yan bindigar daga jihar Kano.

Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin da ke da kwanciyar hankali a arewacin Nigeria, amma a cikin watan Maris 'yan fashi suka kai hari wasu kauyukka hudu inda suka hallaka mutane fiye da 100.

Karin bayani