Ana gab da samar da rigakafin cizon sauro

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ana gab da samarda rigakafin zazzabin cizon sauro

Masu binciken kimiyya a Amurka sun ce sun kusan samar da riga kafin zazzabin cizon sauro.

A wani yanki a kasar Tanzania inda zazzabin cizon sauro ya yi katutu, masu binciken da suka wallafa sakamakon binciken na su a mujallar kiwon lafiya ta Science, sun ce sun samu wasu gungun yara da ba sa kamuwa da cutar.

Gwajin da aka yi ya gano cewa wasu kwayoyin da suke kare garkuwar jikin dan Adam su ke fitar da wani sinadari da ke hana yaran kamuwa da cutar.

Kuma da aka sanyawa beraye irin wannan sinadarin sai aka gano cewa su ma berayen sun samu kariya daga cutar zazzabin cizon sauron.

Sai dai masu binciken kimiyyar sun ce ana bukatar karin gwaji akan birai da mutane domin tabbatar da ingancin riga kafin.

Karin bayani