Shirin makamashin nukiliyar Iran

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tehran ta sha nanata cewa shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya ne.

Hukumar da ke sa ido kan makamashin nukiya ta MDD wato IAEA ta ce Iran ta dakatar da kera kusan kashi tamanin cikin dari na ayyukanta na makamashin Nukiya masu hadari.

A ran nuclear weaponwani bangare na amfani da yarjejeniyar da aka cimma da kasashe shida masu karfin fada aji kan shirin na ta.

A wani rahoto na sirri da BBC ta gani, hukumar sa'idon da ke Vienna ta kara da cewa a karon farko cikin shekaru shida Iran na aiki tare da hukumar domin gudanar da bincike kan zargin ta na kera makamin Nukiliya.

Wakilin BBC a Vienna yace da alama kasashe masu fada aji na duniya za su yi mahabin da wannan sabon rahoto domin cimma yarjejeniya da Iran.

A bangare guda kuma Tehran ta sha nanata cewa shirinta na makamashin Nukiya na zaman lafiya ne.