An kama 'yan adawa 40 a Nijer

'Yan sanda a Jamhuriyar Nijer sun kama 'yan hamayya 40 da kuma dalibai 72 a kasar.

Ministan cikin gida, Malam Hasumi Masa'udu, ya ce an kama su ne akan zarge zargen da suka shafi batun tsaro.

Dukkan 'yan adawan da aka kaman dai magoya bayan jam'iyyar Moden Lumana ne ta shugaban majalisar dokokin kasar Malam Hama Amadu.

Gwamnatin na zarginsu ne da hannu a cikin rigingimun da kasar ke fuskanta wadanda suka hada da hare haren da aka kai a gidan mataimakin shugaban majalisar dokokin, Malam Ben Omar Mohamed, da kuma cibiyar jam'iyyar PNDS Tarayya, mai mulkin kasar.

Haka nan kuma ministan ya tabbatar da kame dalibai 72 sakamakon zanga zangar da suka yi a cikin wannan makon.

'Yan adawa dai sun yi zargin cewa gwamnati ce ke haddasa rigingimun da suka addabi kasar.

Karin bayani