Najeriya: An sake kai wani harin bam a jos

Hari bam a Jos Jihar Filato Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hari bam a Jos Jihar Filato Najeriya

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato a Nijeriya na cewa an sake samun fashewar bam a kusa da wani gidan kallo dake birnin.

Fashewar ta abku ne yayin da masoya kwallon kafa suka hallara suna kallon wasan karshe na Gasar Kofin Zakarun Nahiyar Turai tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid.

Bayanai na cewa bam din ya fashe a wata mota da aka ajiye, wasu bayanan kuma ke cewa maharin ya yi kokarin jefa bam din ne daga mota amma lamarin shi ma ya rutsa da shi.

To sai dai bam din bai shafi gidan kallon ba, amma ya yi kaca-kaca da wani gini dake kusa.

Jami'in tsare-tsare na Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya wato NEMA, a shiyar arewa ta tsakiya ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, amma ya ce suna ci gaba da aikin ceto da kuma tattara bayanai.

Amma wasu shaidu sun ce sun ga gawawwakin mutane akalla hudu baya ga wadanda suka jikkata.

Harin ya zo ne kwana hudu bayan da wasu bama-baman da aka dasa a motoci suka kashe mutane fiye da dari a tsakiyar birnin na Jos yayin da jama'a ke cin kasuwa.