An kashe mutane 20 a Jihar Taraba

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga Karamar Hukumar Wukari ta Jihar Taraba dake arewa maso gabacin Najeriya sun ce kimanin mutane 20 sun rasa rayukansu a wani tashin hankali da aka yi a garin Chinkai.

An dai dade ana fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini tsakanin 'yan kabilar Jukun a bangare daya da kuma Fulani da Hausawa a gudan bangaren.

Bayanai sun nuna cewa an kona gidaje da dama yayin da dimbin jama'a suka kaurace wa garin na Chinkai, domin gudun hijira. An kuma ce hasarar rayuka ta yi muni.

Mazauna garin Hausawa da Fulani na zargin cewa matasan 'yan kabilar Jukun ne suka kai masu harin, wanda ya zo yayin da aka tura karin 'yan sanda zuwa yankin da nufin rigakafin tashin hankali sakamakon zana zullumi da dama ake ciki a yankin.

Wani mazaunin garin mai suna Malam Hussaini ya yi zargin cewa wasu Jukunawa matasa ne su ka kai masu hari.

To amma shugaban matasan kabilar Jukun a Karamar Hukumar Wukari, Mista Zando Hoku, ya musanta hannun Jukunawa a harin.

Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar ta Taraba, DSP Joseph Kwaji, ya ce suna bincike domin sanin takamaiman abin da ya faru.

Karin bayani