An kashe mutane fiye da 20 a Borno

Rahotanni daga Najeriya sun ce wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kauyen Kamuya dake Karamar Hukumar Biu ta Jihar Borno, inda suka kashe mutane sama da 20.

Mazauna wajen sun ce maharan sun shiga kauyen ne a kan babura dauke da bindigogi, suka kuma tare hanyar shiga kauyen suka yi ta harbin mutane.

An ce a yanzu haka dai mutanen kauyen sun gudu saboda fargabar sake kai musu wani harin.

Wani mazaunin kauyen ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa 'yan bindigar sun taba kai masu hari a baya.

Hukumomi dai basu ce komai ba akan lamarin.

Jihar Borno na daga cikin jihohi ukku dake karkashi dokar ta-baci, wadda aka kafa tun bara saboda hare haren 'yan Boko Haram -- sauran jihohin biyu sune Yobe da Adamawa.

'Yan Boko Haram, wadanda suka kame 'yan mata fiye da 200 daga makarantar sakandare ta Chibok dake Jihar Bornon, suna da karfi sosai a jihar.

Karin bayani