Paparoma ya yi kiran kafa kasar Falasdinawa

Paparoma Francis Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Paparoma Francis

Paparoma Francis ya yi addu'a a jikin dogon bangon da Isra'ila ta gina, ta zagaye yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da shi.

Ya yi kira ga Falasdinawa da Isra'ila da su kawo karshen tashin rikicin da ke tsakaninsu, wanda ya bayyana da, wanda yake kara zama abin da ba ba za a amince da shi ba.

Ya ce, "Lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen wannan hali da ake ciki, wanda ke kara zama abin da ba za a amince da shi ba, yadda kowa zai ji dadi.

"Lokaci ya yi da kowa za a sami karfin hali da karimci da kuma hazakar da zai bi hanyar wanzar da zaman lafiya.

Sannan ya yi kira ga duka Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da na Isra'ila, Shimon Perez, da su hadu su yi addu'a tare ta samun zaman lafiya.