Ukraine: Za a fara zaben shugaban kasa

Shirye-shiryen zabe a kasar Ukraine Hakkin mallakar hoto
Image caption Shirye-shiryen zabe a kasar Ukraine

Al'ummar kasar Ukraine za su kada kuri'unsu a zaben Shugaban kasar da aka bayyana abu mafi muhimmanci da ya taba faruwa a tarihin kasar.

'Yan takara 18 ke fafatawa a zagayen farko na zaben da za a yi a yayinda sojojin gwamnati ke cigaba da gwabza fada da 'yan aware magoya bayan Rasha dake gabashin kasar.

Idan har ya zamo ba a samu wanda ya yi nasara a zagayen farko na zaben ba, za a yi zagaye na biyu cikin makonni biyu masu zuwa.

Mutumin da ya yi nasara a zaben, zai fuskanci jan aiki na hada kan mutanen kasar, tare da kawo karshen rikcin da 'yan kwanakin baya-bayan nan ya l;akume rayukkan a kalla mutane 20.