Apple zai sake shari'a da Samsung

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Apple na son a kara yawan diyyar da kamfanin Samsung zai biya shi

Kamfanin Apple ya bukaci a sake duba hukuncin da wata kotu a California ta zartar inda ta umarci Kamfanin Samsung ya biya shi diyyar dala miliyan 119 saboda satar fasahohinsa biyu.

Apple dai ya sha neman Samsung ya biya shi diyyar dala biliyan 2.2 bisa zargin satar masa wasu fasahohi 5 da suka hada da bude waya ta hanyar shafar fuskar wayar.

Kamfanin kasar Amurkan ya sake shigar da wata karar inda ya bukaci a dakatar da Samsung daga yin amfani da fasahohin manhajarsa da ya sata.

Sai dai shi ma kamfanin Samung ya gabatar da wasu takardu ga kotu amma ba a bayyana abin da suka kunsa ba.

A Shari'ar farko da aka gabatar, Apple na zargin Samsung da sace masa manhajojin da suka hada da iOS, yayin da a gefe guda kuma Samsung ke cewa Apple ne ke satar fasaharsa.

Alkalin kotun ya gano cewa, Apple ke da laifi, saboda haka ya umarci ya biya Samsung diyyar dala dubu 158,000 ga kamfanin kasar Korea ta kudu.

'Kai komen Shari'a'

Hakkin mallakar hoto AFP

Sai dai duk da cewa alkalin ya gano wasu fasahohin Apple 2 da aka sata, amma diyyar da ya umarta a biya kamfanin na Apple kalilan ce idan aka yi la'akari da abin da kamfanin Apple din ya nema a biya shi.

Alkalin ya ce," adadin kudaden da Apple ke bukata akwai rinto ciki . Samsung ya ki amincewa inda ya ce kamata ya yi ace kudaden sun yi kasa sosai da dala biliyan 2.2 tun da wasu daga cikin Manhajar ba a yi amfani da su ba.

Matakin shari'ar baya-bayan nan da Apple ke neman dauka na a kara yawan diyyar da aka biya shi, hakan na bukatar sake sabuwar shari'a.

Wani mai fashin baki kan al'amuran da suka shafi kayayyakin fasaha, Florian Mueller, ya ce alkalin na iya yin wasu kananan gyare-gyare kan hukuncin, amma kuma zai ba da dama ga bangarorin biyu na iya daukaka kara a kotun koli.

Wadannan bukatu da Apple ta yi na daga cikin rikicin shari'ar kayayyakin fasahohi da manyan kamfanonin kera wayoyin hannu biyu na duniya ke yi tun cikin shekarun da suka gabata.

Shekaru biyu da suka shude, wani alkali ya umarci Samsung da ya biya Apple dala miliyan 930 bayan samun sa da laifin satar fasahar Apple, amma Samsung ya kalubalanci wannan hukunci.