Gangamin #BringBackOurGirls ya yi kishiya

'Yan Grand Alliance Against Terrorism Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yekuwar 'yan Grand Alliance Against Terrorism ita ce a yi tir da 'yan ta'adda

Asali jajayen riguna suke sanyawa, kuma bukatarsu ita ce gwamnati ta kara zage dantse, suna kuma amfani da jigon #BringBackOurGirls.

Wadannan su ne masu fafutukar matsin lamba ga gwamnatin Najeriya ta dauki kwararan matakai don dawo da 'yan matan da kungiyar Boko Haram ta sace daga makaranatrsu a garin Chibok na arewa maso gabashin kasar.

Kwatsam sai aka fara ganin wadansu mutane su ma da jigon na #BringBackOurGirls, amma su da fararen kaya.

Wadannan 'yan wata sabuwar kungiya ce mai suna Grand Alliance Against Terrorism, wadda ta ce kamata ya yi hankali ya koma wajen yin tir da kungiyar Boko Haram maimakon sanya gwamnatin Najeriya a gaba ana azalzalarta cewa sai ta kubuto da 'yan matan sakandaren Chibok.

'Yan asalin gwagwarmayar #BringBackOurGirls din dai a nasu bangaren sun ce babu abin da ya sha musu kai da wanzuwar wannan sabuwar kungiyar.

Wasu na zargin cewa gwamnatin Najeriya ce ta baiwa 'yan Grand Alliance Against Terrorism kudi sama da nara miliyon dari da hamsin don ta nemo 'yan are-ni-mu-je-biki domin su bata tafiyar ta #BringBackOurGirls.