Ana zaben shugaban kasa a Masar

Zaben shugaban kasa a Masar Hakkin mallakar hoto .
Image caption Zaben shugaban kasa a Masar

Misirawa sun fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa, inda tsohon hafsan soji Abd-alFatth-al-Sisi da Hamdin Sabahi za su fafata.

An yi ta kiraye-kiraye ga 'yan kasar ta Masar da su fito su kada kuri'unsu don maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Sai dai kungiyar 'yan uwa musulmi da Jam'iyar tsohon shugaba Mohammed Morsi da aka tumbuke a bara, ke kan gaba wajen yin kiran a kauracewa zaben.

Haka ma wasu dumbin matasa masu ra'ayin juyin juya hali na neman jama'a su nisanci rumfunan zaben.