Nijar da Areva sun kulla 'yarjejeniya

Kamfanin hako ma'danin uranium na Areva Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Areva da hukumomin Nijar sun sanya hannu a yarjejeniyar ne a Yamai

Kasar Nijar da kamfanin Faransa na AREVA sun kulla sabuwar 'yarjejeniya inda kamfanin Areva zai kara harajin da yake biyan Nijar.

Kamfanin zai biya harajin kashi 12 cikin dari na kudaden ma'adanin uranium ga hukumomin Nijar, maimakon kashi biyar da digo biyar da yake biya.

Haka kuma ya amince ya kashe euro miliyan 90 wajen gina hanyoyin da za su kai ga mahakar ma'adanan, tare da kashe euro miliyan 17 wajen ayyukan inganta rayuwar al'umar yankin da kamfanin yake.

Bangarorin biyu sun kwashe shekaru biyu suna ja-in-ja gabannin karewar tsohuwar yarjejeniyar a watan Disambar 2013.

Jinkirin ya biyo bayan dagewar da hukumomin Nijar suka yi cewa sai an yi amfani da dokar hakar ma'adinai ta shekara ta 2006 wajen sabunta 'yarjejeniyar.

Yayin da kamfanin na AREVA ke ganin hakan zai yi mummunan tasiri a kan kudaden shigar da yake samu.