Poroshenko ne sabon shugaban Ukraine

Petro Poroshenko Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Poroshenko ya ce yana son kawo karshen tashin hankali a gabashin Ukraine

Hukumar zabe ta kasar Ukraine ta tabbatar da nasarar Petro Poroshenko a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar.

Jami'ai sun ce ya sami kashi hamsin da hudu cikin dari na kuri'un da aka kada.

Mr Poroshenko hamshakin atttajiri kuma tsohon Ministan harkokin waje ya ce yana son ganin kawo karshen boren magoya bayan Rasha a gabashin kasar, amma ya ce ba zai tattauna da wadanda ya kira yan ta'adda ba wadanda ke neman maida gabashin Ukrain tamkar wata Somalia.

A waje guda kuma jiragen yaki na soji masu saukar ungulu sun kai hari filin saukar jiragen sama a Donetsk a gabashin Ukraine din a kokarin sojan gwamnati na karbe iko da shi, bayan da 'yan bindiga 'yan aware suka kama shi da sanyin safiyar Litinin.

Karin bayani