EU na bukatar sauyi - Hollande

Kungiyar Trayyar Turai Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Trayyar Turai

Shugaban kasar Faransa Franswa Holland ya yi kiran da a gudanar da sauye-sauye a tsarin Tarayyar Turai bayan jam'iyyun dake adawa da hadewar Tarayyar Turan sun samu gagarumar nasara a zaben da aka gudanar na majalisar dokokin kungiyar da ta hada kasashe 28.

Gabanin wani taro da za su yi nan gaba a yau Talata a Brussels, Mr Holland ya ce, tsarin Tarayyar Turan na da ne kuma yana da wuyar fahimta ga 'yan kasashen, yace, yakamata alkiblar kungiyar ta zamo ta bunkasa tattalin arziki.

Ya yi maganar ne bayan jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayin 'yan mazan jiya "The Front National" ta cinye zabukan tarayyar Turai a Faransa da kimanin kashi daya bisa ukku na kuri'un, ta tura jam'iyyar Socialist ta Mr Holland a matsayi na ukku.

Karin bayani