Modi ya nemi Pakistan ta hana kai hari Indiya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr. Modi ya tattauna da wasu shugabannin kasashen da ke makwabtaka da Indiya, tun bayan bikin rantsar da shi

Wani jami'i a Indiya ya ce Firai minista Nerandra Modi, ya shaida wa takwaransa na Pakistan Nawaz Sharif cewa, tilas Pakistan ta hana 'yan bindiga kai hare-hare a Indiya.

Jami'in a ma'aikatar wajen kasar ya bayyana cewa Mr. Modi ya ce akwai yiwuwar kasashen biyu su kyautata huldar cinikayya a tsakaninsu.

A nasa bangaren Nawaz Sharif ya ce yana fatan ya yi aiki da Mr. Modi, domin kawar da matsalar rashin tsaro a yankin.

Dangantaka tsakanin Indiya da Pakistan ta yi tsami, bayan harin ta'addancin da aka kai Mumbai shekaru shida da suka wuce, harin da mutane 166 suka mutu.

Karin bayani