Doka kan canza addini a Myanmar

Image caption Shugaban kasar Myanmar, Thein Sein

Gwamnatin kasar Myanmar na shirin kafa wata doka da za ta tilastawa mutum neman izinin gwamnati kafin ya canza addininsa.

Kudurin dokar da kungiyoyin mabiya addinin Budha ke goyon bayan, ya biyo bayan rikicin kin jinin Musulmai a kasar, lamarin da ya janyo mutuwar dubbai a yayinda wasu dubun dubatan suka rasa ayyukansu.

Ma'aikatar harkokin addini a kasar ta Myanmar za ta kafa kwamitoci a cikin al'umma domin duba batun na masu kokarin canza addininsu.

Mabiya addinin Budha na son a tsaurara matakai a kan al'umma Musulmi marasa rinjaye a kasar saboda batun rikicin addini da kasar ke fuskanta.

Karin bayani