Niger ta kulla yarjejeniya da kamfanin AREVA

Mahakar ma'adinan Uranium ta Areva Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mahakar ma'adinan Uranium ta Areva

Jumhuriyar Nijar da kamfanin makamashi na Faransa AREVA, sun kulla sabuwar 'yarjejeniyar ci gaba da hako ma'adanin Uranium a kasar.

Tun a karshen watan Disambar bara ne dai 'yarjejeniyar dake tsakanin bangarorin 2 ta kawo karshe, amma ba su samu damar sabunta ta ba.

Hakan ya faru ne saboda gwamnatin Nijar din ta dage kan cewa dole ne a yi aiki da dokar da ta shafi hakar ma'adinai ta shekara ta 2006 wajen sabunta 'yarjejeniyar.

Tuni dai kungiyoyin farar hula a Nijar din suka fara tofa albarkacin bakinsu game da wannan 'yarjejeniya.