Hukuncin kisa kan dan Shi'a a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Wata kotu a Saudi Arabia ta yanke wa wani dan babban malamin Shi'a hukuncin kisa saboda harbin 'yan sanda lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnati a gabashin kasar shekaru uku da suka wuce.

Rida al-Rubh dan Sheikh Jafaar al-Rubh, wanda ke cikin masu sulhu tsakanin al'ummar 'yan Shi'a da kuma gwamnatin Saudiyya sakamakon zanga-zanga a garin Awamiya a shekara ta 2011.

Masu aiko da rahotanni sun ce wannan hukunci shi ne mafi tsauri da aka yanke cikin shari'ar da ake yi wa mutanen da suka gudanar da zanga-zanga a Saudiyya.

A lokacin dai an damke masu zanga-zanga fiye da 900, kuma a halin yanzu akwai kusan 300 da ke tsare a hannun hukuma.

Karin bayani