'Yan Sudan ta Kudu 70,000 sun tserewa rikici

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rikici tsakanin shugaba

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kimanin mutane dubu 70 ne suka tserewa rikicin Sudan ta Kudu.

Mutanen sun tsere ne daga jihar Jonglei da ta Upper Nile, bayan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta makonni uku da suka wuce.

Hukumar ta kara da cewa akalla mutanen Sudan 1000 ne ke shiga Habasha, inda a yanzu kasar ke neman gurin na hudu da za ta tsugunar da su.

An yi gargadin samun matukar karancin abinci a Sudan ta Kudun, wadda fadan da ake yi ya taimaka wajen haddasa shi.

Karin bayani