Ridda: 'Yar Sudan ta haihu a Kurkuku

Image caption Matar da mutumin da ta aura

Lauyoyin 'yar kasar Sudan da aka yanke wa hukuncin kisa bisa zargin ta yi ridda, sun ce ta haihu a kurkukun da ake tsare da ita.

Matar, wadda ta auri wani kirista, a farkon watan nan ne wata kotu a Khartoum, babban birnin kasar ta same ta da laifi, bayan da ta ki ta ce ita ba Kirista ba ce.

Kotun ta yanke ma hukuncin ratayewa har sai ta mutu, shekaru biyu bayan ta haihu.

Ita dai matar ta taso ne a hannu wasu Kiristoci, amma ake daukarta Musulma saboda mahaifinta musulmi ne, duk kuwa da cewa ba a gabansa ta tashi ba.

Sannan kuma an same ta da laifin aikata zina saboda mata musulmi haramun ne su aure mazan da ba musulmai ba.