Chibok:Amurka na tababar ikirarin Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Babban hafsan dakarun Nigeria, Air Marshal Alex Badeh

Amurka ta ce ba ta da bayani mai zaman kansa da ke tabbatar da cewar an san inda 'yan matan Chibok da aka sace suke.

Kakakin Ma'aikatar harkokin kasashen wajen Amurka, Jen Psaki ta ce "Bamu da bayanai masu zaman kansu game da ikirarin cewar an san inda 'yan matan suke".

Babban hafsan dakarun tsaron Nigeria, Air Marshal Alex Badeh a ranar Litinin ya bayyana cewar rundunar tsaron kasar ta ce ta san inda ake tsare da 'yan mata fiye da 200 da kungiyar Boko Haram ta sace a jihar Borno.

Amma kuma Badeh ya ce ba za su yi amfani da karfi ba wajen kubutar da 'yan matan wadanda ke hannun 'yan Boko Haram fiye da makonni shida da suka wuce.

Jen Psaki ta kara da cewar "A cikin tsarinmu da kuma batun lafiya da kariyar 'yan matan, ba zamu yi magana a bainar jama'a ba a kan bayanai irin wadannan".

Kasashen Amurka da Birtaniya da China da Faransa da kuma Isra'ila suna taimakawa Nigeria a kokarin kubutar da 'yan matan na Chibok.

Karin bayani