Ana Jimamin rasuwar Sarkin Gombe a Nigeria

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, ana ci gaba da jimanin rasuwar Mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Shehu Usman Abubakar, da ya rasu da safiyar Talata a birnin London.

Kafin rasuwarsa shi ne kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Gombe da ke arewacin kasar.

Tuni dai aka soma mika sakonnin ta'aziya, inda kakakin majalisar wakilai ta Nijeriya, Alhaji Aminu waziri Tambuwal ya bayyana marigayi Sarkin Gombe a matsayin mutum mai tsayin daka kan manufofinsa da akidarsa.

Kafin ya zamo sarki a cikin watan Janairun 1984, Marigayi Alhaji Shehu Usman Abubakar ya yi aikin gwamnati a matakai daban-daban.

Ya rasu yana da shekaru 76 da haihuwa, kuma ya shafe kimanin shekaru 30 a kan gadon sarauta a matsayin sarkin Gombe na goma, bayan ya gaji mahaifinsa Abubakar Umar Farouk.