Obama ya shata sabon babi a manufofin wajen Amurka

Shugaba Obama a Westpoint Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Obama a Westpoint

Shugaba Obama ya zayyana irin abubuwan da yake fatan ganin sun kasance game da manufofin harkokin wajen Amurka, yayinda take bude wani sabon babi.

Ya bayyana haka ne a wata makarantar soja dake West Point, lokacin bikin yaye dalibai, yana mai cewa ya zama wajibi Amurka ta ci gaba da jagoranci a duniya, amma ba kawai da karfin soja zata yi haka ba.

Shugaba Obama ya ce, ta hanyar taimakawa wadanda ke gwagwarmayar samar da 'yanci ga al'umar Syria, suna kuma kauce ma fadawa tarkon wasu masu tsaurin ra'ayi dake kara samun wurin zama a Syriar.

A jawabin nasa Mr Obama ya kare matakin da ya dauka na kin tsoma baki a Syria ta karfin soja, amma ya bada sanarwar bada karin taimako ga 'yan adawar Syria domin su yi gwagwarmayar samar wa da kansu makoma.