Kungiyar Taliban ta rabu gida biyu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan Taliban a Pakistan

Kwamandan daya daga cikin bangarorin kungiyar Taliban ta Pakistan ya ce a yanzu sun balle daga uwar kungiyar.

Azam Tariq, kakakin bangaren Mehsud na kungiyar Tehrik-i-Taliban wadda aka haramta a Pakistan, ya bada sanarwar cewa kungiyarsa ta TTP ta balle daga babbar kungiyar.

Azam Tariq ya shaidawa manema labaru a yankin Waziristan ta Kudu cewa za su bar kungiyar ne saboda sabanin ra'ayin da aka samu a tattaunawar sulhun da ake yi da gwamnati.

Mr Tariq ya ce kungiyarsa na goyon bayan tattaunawar, amma shugabannin kungiyar ta Taliban na son a ci gaba da kai hare-hare kan gwamnatin.

Karin bayani