Gwamnatin Nigeria ta gaza ta fuskar tsaro

BringBackOurGirls
Image caption BringBackOurGirls

A Najeriya Kungiyar BringBackOurGirls, mai neman a ceto da 'yan matan da 'yan Boko Haram suka sace daga wata makarantar sakandare, ta shirya wani taron wayar da kan jama'ar kasar a kan hakkokinsu da ke wuyan gwamnati.

Kungiyar ta BringBackOurGirls tana gaba-gaba wajen matsa wa gwamnatin Najeriya lamba don ta ceto 'yan matan Chibok su sama da dari biyu.

Kungiyar ta kira masana ne don su gabatar da laccoci a kan hakkin jama’ar a kan gwamnati da kuma hakkin gwamnatin a kan ‘yan kasa.

Kwararru a wurin taron, ciki har kwararren masanin dokar tsarin mulki, Farfesa Awwalu Yadudu, sun ce samar da tsaro ga dan kasa yana daga cikin hakkokin da ke wuyan gwamnatin.

Sun kuma nuna a Najeriyar, hakkin tsaro yana wuyan gwamnatin tarayyar kasar ne, tunda ita ce ke da soja, da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro.

Saboda da haka ‘yan kasa suna da ikon neman gwamnati ta yi masu bayanin matakin da take dauka dangane da tsaron.

.