Fyade: 'Yan sanda India sun yi kame

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bishiyar da aka rataye 'yan matan

'Yan sandan India sun ce, sun kama wani mutum kana suka shigar da wasu mutanen da dama kara dangane da mummunan fyaden da ya kai ga kisa da aka yi wa wasu 'yan mata biyu a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin kasar.

'Yan matan biyu da aka yi wa fyaden sun fito ne daga zuri'ar mutanen da ake dauka da kasakanci, an samu gawarwakinsu ne a rataye a jikin bishiya da safiyar ranar Laraba.

Mazauna kauyen da lamarin ya auku sun ce, da farko dai 'yan sanda sun ki yarda su bincika lamarin har sai da mutanen kauyen suka yi amfani da gawarwakin matan biyu wajen yin zanga-zanga a kan batun.

Tuni dai aka dakatar da wasu jami'an 'yan sanda uku saboda rashin daukar mataki nan take a kan lamarin.

Karin bayani