'Mun daura damarar yaki da Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Shugaban Nigeria Dr Goodluck Jonathan ya umurci sojojin kasar da su kaddamar da yaki gadan-gadan da kungiyar Boko Haram.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi wa al'ummar kasar na bikin ranar dimokradiyya.

Shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana cewa mulkin Dimokradiyyar a Najeriya, wanda ya cika shekara goma sha biyar da sake kafuwa na fuskantar barazanar gaske daga musamman hare-haren ta'addanci, don haka gwamnatinsa ba za ta zuba ido wa wasu har zuwa lokacin da za su gama kassara dimokradiyyar ba.

Kuma wannan ne ya sa ya umurci sojan kasar da su bi duk wata hanyar da za ta taimaka wajen yakar kungiyar Boko Haram.

Ya ce "Babu shakka abin da ke faruwa a Nigeria ba shi da bambanci da abin da ya faru a Amurka lokacin da aka kai harin da ya ka da tagwayen benayen nan biyu a New York, inda mutane da dama da ba su ji ba ba su gani ba suka mutu".

'Ceto 'yan matan Chibok'

Kazalika shugaban kasar ya sha alwashin ci gaba da kokarin ceto 'yan matan nan na makarantar Sakandaren Chibok daga hannun kungiyar Boko Haram.

Mr Jonathan ya ce "Kwana 45 kenan da sace 'yan mata 'yan makarantar sakandaren Chibok, lamarin da ya jefa al'umar Najeriya da sauran kasashen duniya cikin juyayi".

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan matan Chibok da ke hannun 'yan Boko Haram

Ya kara "Don haka ya ce yana taya iyayen wadannan yara bakin ciki tare da jin takaicin da suke ji. Har ma ya tabbatar musu cewa gwamnati za ta yi bakin kokarinta wajen ganin 'ya'yan nasu sun koma gida".

Umurnin da Shugaba Jonathan ya baiwa sojoji na yin fito-na-fito ko karon-batta da 'yan kungiyar Boko Haram din dai ta wata fuska yana da harshen damo.

Saboda yayin da yake cewa sojoji su bi duk wata hanyar da za ta taimaka wajen murkushe kungiyar, shugaban kasar ya sake cewa har yanzu gwamnatinsa a shirye take ta yi tattaunawar sulhu da kungiyar.

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Gangamin Bring Back Our Girls
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Taron yaki da Boko Haram a Paris

Karin bayani