An jefe mai ciki har ta mutu a Pakistan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mahaifinta ya ce bai yi nadamar kashe 'yar tasa da suka yi ba.

Kwamishinar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay, ta yi tir da kakkausan lafazi da kashe wata mata mai juna biyu da danginta suka yi a kasar Pakistan.

An dai kashe Farzana Parveena ne a harabar wata kotu a birnin Lahore saboda ta auri wani mutumin da take so amma danginta ba su son sa.

Mamaciyar dai ta je kotun ne tare da mijin nata Muhammad Iqbal domin kare shawarar da ta yanke ta auren sa bayan iyayenta sun kai shi kara suna zarginsa da sace ta.

Daruruwan mata ne ake kashewa a kasar ta Pakistan da sunan kare martabar gida, sai dai wannan ya fusatar da jama'a sosai.

Karin bayani