Bidiyo: Sojin Nigeria sun nisanta kansu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rundunar sojin kasar ta sha musanta zarge-zarge kisan fararen hular da ake yi mata

Shalkwatar tsaron Najeriya ta ce ta gano wani shiri da wasu ke yi na bata wa rundunar sojin kasar suna domin janyo kasashen duniya su yi tur da ita.

Rundunar ta ce ana amfani da wasu hotunan bidiyo da muryoyi da aka nada aka kuma gurbata su, wadanda ke yawo a shafukan sada zumunta domin cimma wannan manufa.

Shalkwatar tsaron Najeriyar ta kuma ce tana zargin wani dan siyasa a daya daga cikin jihohin da ke karkashin dokar ta baci da samar da kudaden da ake amfani da su wajen bata wa sojojin suna.

A faifan bidiyon da rundunar ke korafi a kai an nuna wasu mutane, har da masu sanye da kakin soji, suna yanka mutane a kusa da wani rami.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da bidiyon da ake zargin sojoji da aikata kisan gilla ke yawo a shafukan sada zumunta.