'Yan bindiga sun kashe Sarkin Gwoza

Hakkin mallakar hoto Isa Gusau
Image caption Sarkin Gwoza, Alhaji Shehu Idriss Timta

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe Sarkin Gwoza Alhaji Shehu Idriss Timta a jihar Borno.

Sarkin ya rasa ransa ne a harin da aka kai wa tawagar Sarakunan Askira da Uba da na Gwozan a kan hanyarsu ta zuwa jihar Gombe, domin yin ta'aziyyar Sarkin Gombe.

Lamarin na ranar Juma'a ya faru ne a garin Tashar Alade da ke karamar hukumar Hawul a gundumar Biu, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Gombe domin yin ta'azziya a kan rasuwar Sarkin Gombe.

Zannan Gwoza, Alhaji Wali Ibrahim ya shaidawa BBC cewar "Mun taso zamu je jana'iza a Gombe, akwai Sarki Askira, akwai na Gwoza akwai Sarkin Uba, mun bar Gumbi zamu nufi Biu a daidai tashar alade sai 'yan bindiga suka fito daga saman dutse suka bude mana wuta".

Ya kara da cewar "Bayan da muka bar wurin, sai ba muga Sarkin Gwoza ba, da muka koma sai muna tarar an kashe shi. Allah ya yi masa rasuwa".

Rahotanni sun ce Sarkin Askira, Mai martaba Alhaji Bala Askirama da Sarkin Uba Mai Martaba Ali Isma'ila Mamza suna nan lafiya.

Tuni dai matasa na garin Gwoza, wadanda suka tasamma 40, suka ce a shirye suke su kai dauki wurin da abun ya faru.

Wani na kusa da fadar mai martaba Sarkin Gwoza ya ce suna kan hanyarsu ta zuwa garin da harin ya auku domin tantance ainihin abinda ya faru.

A baya 'yan Boko Haram sun kai hari a kan Sarkin Kano da Shehun Borno da Sarkin Fika.

Karin bayani