Amurka ta nuna damuwa kan Ukraine

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ukraine dai na zargin Rasha ta kitsa makircin afkuwar tashin hankalin.

Fadar Gwamnatin Amurka ta nuna damuwa kan yadda ta ce mayakan sa-kai masu goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine na amfani da manyan makamai a yakin da suke.

Wannan ya biyo ne bayan harbo wani jirgin sojan Ukraine da suka yi ranar Alhamis a kusa da garin Slovyansk da wani makami mai linzami kirar Rasha; abin ya hallaka Sojoji Goma 12.

Mai magana da yawun fadar ta White House Jay Carney ya ce haka ma Amurka ta damu da yadda 'yan aware a gabashin Ukraine din ke ci gaba tsare masu sa-ido daga kungiyar wanzar da tsaro da hadin kai a nahiyar Turai wato OSCE.

''A halin yanzu ba zamu iya tanttance wadannan rahotannin ba, amma dai mun damu ganin cewar wannan na nuna yadda 'yan aware ke ci gaba da samun manyan makamai da kuma taimako daga waje,'' inji kakakin na fadar White House.

Karin bayani