Amodo Boudou zai bayyana gaban Kuliya

Mataimakin shugabar kasar Argentina Amodo Boudou Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mr boudou dai ya bawa kamfanin da ya saya kwantiragin buga kudaden kasar ta Argentina

Mai shari'a a kotun Argentina ya aikawa mataimakin shugaban kasar Amodo Boudou sammacin ya bayyana a gaban kotun a cikin watan Yuli domin ya kare kanshi daga zargin almundahana da ake masa.

Wakilin BBC ya ce tun a shekarar 2010 ake gudanar da binciken.

Inda ake zargin Mr Boudou da sayan wani kamfanin buga takardu da ya riga ya tsiyace,.

Tare da amfani da mukaminsa wajen ba wa kamfanin kwantiragin buga takardun kudin kasar ta Argentina.

Sai dai Mr Boudou, wanda ake ganin shi zai gaji shugaba Cristina Farnandez yace zai tabbatar da gaskiyarsa idan ya bayyana a gaban kotu a ranar 15 ga watan Yuli.