Hagel ya gargadi Sojojin Thailand

Shugaban sojin Thailand da ke jan ragamar kasar a yanzu Gen Prayuth Chan-ocha Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Janal Prayuth dai shi ya jagoranci juyin mulkin da aka yi a kasar thailand a makon da ya gabata, bayan an tsige Prime minista Shinawtra daga mukamin ta.

Sakataren ma'aikatar tsaron Amurka Chuck Hagel, ya yi kira ga shugabannin sojin Thailand da su dawo da dimukradiyya kasar nan ba da jimawa ba.

Da yake jawabi a wurin taron harkokin tsaro a Singapore, Mr Hagel ya bukaci sojojin su kawo karshen hana fadar albarkacin baki, da sako fararen hula da suke tsare da su kana su dawo da mulki hannun farar hula ta hanyar gudanar da Zabe.

Ya yi wannan jawabi ne mako guda da hambarar da gwamnatin kasar, bayan da aka shafe watanni ana gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na Thailand.

Sai dai tun a jiya juma'a ne sabon shugaban kasar Janal Prayuth Chan-o-Cha a jawabin da ya yi wa al'umar kasar da aka watsa a gidan talabijin, yace Thailand na bukatar lokaci don yin gyara ga Dimukradiyyarta.

Ya kuma ce Za a kafa wata majalisar dokokin da za ta zabi Prime minista, ta nada majalisar ministoci, ta rubuta sabon kundin tsarin mulki kazalika ta kafa wani kwamiti da zai yi sauye-sauye kan abubuwan da al'ummar kasar ke bukata, kuma ga alama yin hakan zai dauki shekara guda.