ECOWAS zata taimaki Najeriya da Mali

Mayakan Boko Haram Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Mayakan Boko Haram

Shugabannin kasashen yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS ko CEDEAO sun yi alkawarin taimakawa Najeriya da Mali domin shawo kan rikice-rikicen da suke fama da su.

Mambobin ECOWAS din sun bayyana hakan ne bayan taron gaggawar da suka gudanar jiya da dare a birnin Accra na Ghana.

Sun kuma ce za su kulla kawance da kasashen yankin tsakiyar Afirka don yaki da ayyukan ta'addanci.

Najeriya ta sha nanata cewa ta na bukatar karin taimako daga makwabtanta na yankin tsakiyar Afirka irinsu Chadi da Kamaru, a yakin da ta kwashe shekaru biyar ta na yi da 'yan Boko Haram.

Kungiyar ECOWAS din ta kuma bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta karfafa rundunar kiyaye zaman lafiyarta da ke kasar Mali.

Shugabanni goma ne suka halarci taron na Accra - ciki har da na Najeriya da Nijar da Mali da kuma Burkina Faso.