'Yan Taliban sun sako sojan Amirka

Sergeant Bowe Bergdahl Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sergeant Bowe Bergdahl

An sako sojan Amirka na karshe da ake tsare da shi a Afghanistan, kusan shekaru biyar tun bayan da 'yan Taliban suka kama shi.

Jami'an Amirkan suka ce, Sergeant Bowe Bergdhal na cikin koshin lafiya.

To amma ya fashe da kuka don murna, bayan da aka mika shi ga sojojin musamman na Amirkan.

An sako Sergeant Bergdhal ne a madadin wasu manyan 'yan gwagwarmaya na Taliban su biyar, wadanda ake tsare da su a sansanin Guantanamo.

Za a kaisu kasar Qatar ne.

Sakataren tsaron Amirka Chuck Hagel, da kuma sakataren harkokin wajen Amirkan John Kerry, sun gode wa gwamnatin Qatar wadda ta taimaka aka cimma yarjajeniyar.