Afghanistan ta soki musayar fursunoni

Hakkin mallakar hoto Getty

Gwamnatin Afghanistan ta maida martani a fusace game da wata yarjajeniyar da Amirka ta kulla, wadda a karkashinta aka mika manyan 'yan Taliban biyar da ke tsare a sansanin Guantanamo ga kasar Qatar a madadin wani sojan Amirka da 'yan Taliban suka kama.

A cewar Afghanistan din, mika fursunonin wata kasa ga wata kasar ta dabam ya keta dokokin kasashen duniya.

To amma jagoran Taliban, Mullah Omar, ya ce sakin daurarrun na Guantanamo babbar nasara ce a garesu.

Sakataren tsaron Amirka, Chuck Hagel, kuma ya kare matakin, wanda ya ce na gaggawa ne saboda rayuwar sojan na cikin hadari.

Mista Hagel ya ce bai san ko wannan musayar zata sa a sami cigaba wajen sasantawa da 'yan Taliban ba. Amma yace yana fatan hakan zai ya faru.

Ga alama dai masu adawa da Shugaba Obama a Amurkan da kuma jami'an gwamnatin Afghanistan ne suke nuna rashin jin dadinsu sosai.

Haka ma wata 'yar majalisar dokokin Afghanistan din, Nahid Farid, ta soki batun.

Tace: "Wannan zai iya zama labari marar kyau ga al'ummar Afgahnistan.

"Barazana ce ga harkar tsaro, kuma na yi ammana barazana ce ga shirin zaman lafiya, saboda bamu da tabbacin cewa zamu iya sanya 'yan Taliban su zauna terburin shawara da mu."