An sako 'yan Italiyan da aka sace a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP

An sako wasu fada-fada biyu 'yan kasar Italiya tare da wata mai hidimar coci 'yar kasar Canada, wadanda wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka sace a watan Afrilu a kasar Kamaru.

Ministan yada labaran Kamarun ya ce dukkan mutanen uku na cikin koshin lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa an sako su ne da kimanin karfe biyu na safiyar Lahadi; aka kuma dauke su ta jirgin sama zuwa birnin Yaounde.

An yi awon gaba da su ne a arewacin Kamaru din kusa da kan iyaka da Najeriya.

A makon jiya, gwamnatin Kamaru ta tura sojoji kimanin dubu guda zuwa iyakarta da Najeriya, domin dakile barazanar da kungiyar Boko Haram ke cigaba da yi a wannan yanki.

Ana dai samun matsalar satar mutane a arewacin Kamarun tun lokacin da 'yan Boko Haram suka fara kai hare-hare a yankin.

A makonnin baya an sace wasu 'yan kasar China dake aiki a arewacin Kamarun bayan da 'yan bindiga suka kai masu hari.

A bara ma 'yan Boko Haram sun sace wani fada da wasu mutane bakwai 'yan kasar Faransa a arewacin Kamarun.

Karin bayani